Soji sun karbi ragamar tsaro daga JTF

Wani sojan Najeriya
Image caption An cire jami'an 'yan sanda dana SSS daga harkar tsaro a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa

Rundunar sojin Najeriya ta karbi ragamar tsaro, a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa, daga hannun rundunar hadin gwiwa ta JTF.

A wata sanarwa da shalkwatar tsaro ta kasar ta fitar, ta ce sauyin wani bangare ne na dokar ta baci, a jihohin uku na arewa-maso-gabashin kasar.

Sabon sashen karkashin manjo janar, zai kasance yana da shalkwata a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A makon jiya ne, Amurka ta ce wajibi ne ga Najeriya ta kara kaimi ta fuskar tsaro, domin kare 'yan kasar daga abin da ta kira zubar da jinin da kungiyar Boko Haram ke yi.