Gwamnatin kasar Masar na kamfe na kafa hujjarta

Sojojin kasa Masar
Image caption Sojojin kasa Masar

Gwamnatin kasar Masar na wani kamfe na kafa hujjarta, game da matakan da jami'an tsaronta suka dauka kan magoya bayan kungiyar 'Yan uwa Musulmi.

Hakan ya biyo bayan kwanakin da aka shafe ana tafka rikici a kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

A wani taron manema labarai a birnin Alkahira, Ministan harkokin wajen kasar Nabil Fahmy ya ce gwamnatin ta fuskanci yunkurin yi mata yankan baya.

Mr Nabil ya ce kasar Masar na da isasshen girman da za ta kunshi kowa.

Ya ce a ko da yaushe a shirye kasar ta ke don jin shawarwari ko martani daga kasashen waje.

Wadannan su ne kalamansa na farko tun bayan da soji suka soma daukar mataki kan kungiyar 'Yan'uwa Musulmi, abin da ya kai ga kisan daruruwan mutane.

Kungiyar EU ta yi gargadi

Kungiyar Tarayyar Turai dai ta gargadi kasar Masar cewa za ta duba yanayin dangantakar su nan da 'yan kwanaki.

Ta kuma ce babu wata hujja kan tashin hankali da kashe-kashe.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce sake sabon zabe ita ce mafita game da wanna rikici.

Mr Hollande ya ce duka kasashen larabawa, Turai da Faransa,na da hakkin da ya rataya a wuyansu, na tabbatar da ganin cewa an dakatar da tashin hankalin.

Ya kuma yi kira da a bai wa mahukuntan siyasar kasar damar daukar matakan fara gudanar da sabon zabe, ta yadda Misirawa za su nuna abinda suke bukata.

A nata bangaren kasar Saudi Arabia, ta yi gargadi ga kasashen yammacin duniya kan matsin lambar da take yiwa gwamnatin kasar Masar na ta daina musgunawa magoya bayan kungiyar 'Yan uwa Musulmi.