Kotu a Masar ta wanke Hosni Mubarak

Image caption Hosni Mubarak

Wata kotu a Masar ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon Shugaban kasar Hosni Mubarak, a kan daya daga cikin laifukan da ake zarginsa da su na cin hanci.

Lauyan Mista Mubarak ya ce nan ba da jimawa ba za a saki tsohon shugaban kasar, idan har aka wanke shi daga daya daga cikin tuhumar da ake masa.

A cewarsa, zargin cin hanci da rashawa ne kawai ya sa ake ci gaba da tsare Mista Mubarak.

Sai dai har yanzu akwai wata shari'ar da zai kara fuskanta a kan hannun wajen kashe masu zanga-zanga lokacin boren da ya hambarar da shi daga kan mulki a shekarar 2011.

Karin bayani