Jamus: 'Yan sanda sun kama ɗan bindiga

Image caption An yiwa dakin taron kawanya

'Yan sanda a kudancin Jamus sun kama wani dan bindiga da ya yi garkuwa da wasu mutane uku a wani zauren taro da ke Ingolshtat.

An yi tsammanin mataimakin magajin garin na cikin wadanda aka yi garkuwa da su, wadanda a halin yanzu aka sake su ba tare da sun yi ko da kwarzane ba.

Kafafen yaɗa labaran Jamus sun ce dan bindigar mai shekaru ashirin da hudu ya yi ta farautar ɗaya daga cikin ma'aikatan da ke kula da zauren taron.

A da dai shugabar Jamus Angela Merkel ta shiryar ziyartar garin na Ingolshtat don halartar wani gangamin siyasa, amma ta fasa bayan faruwar al'marin.