Za'a tuhumi Morsi da ingiza tashin hankali

Masu shigar da ƙara a Masar sun gabatar da sabbin tuhume-tuhume a kan hamɓararren shugaban ƙasar mai ra'ayin addinin musulunci Muhammad Morsi.

Masu gabatar da kara sun ce, za'a tuhumi Morsi ne da laifin rura wutar rikici.

Tuhume-tuhumen na da alaKa da rasuwar mutane da dama yayin zanga-zangar kin jinin gwamnatin Morsi da aka gudanar a kofar fadar shugaban kasa a watan Disamban shekarar da ta gabata.

Ba a dai ga Mr Morsi a bayyanar jama'a ba tun bayan da sojojin kasar suka tsare shi makwanni bakwai da suka gabata.