An tuhumi tsohon shugaban Pakistan

Tsohon shugaban Pakistan Pervez Musharraf
Image caption Tsohon shugaban Pakistan Pervez Musharraf

An tuhumi tsohon shugaban kasar Pakistan, Janar Pervez Musharraf, bisa hannu a kisan tsohuwar Fira Ministar kasar Benazir Bhutto a shekarar 2007.

An dai gurfanar da shi ne gaban wata kotu dake shari'ar aikata ta'addaci a Rawalpindi.

An kuma tuhume shi da hada baki wajen aikata kisa, da rashin samar da isasshen tsaro da kuma lalata takardun shaidar aikata laifi.

Mr Musahrraf dai ya musanta duk wadannan zarge-zarge da ake yi masa tare da wasu mutane shida da aka gurfanar tare da shi.

Sun kuwa hada da wasu mutane biyu da ake zargi da tada kayar baya da kuma wasu manyan jami'an 'yan sanda biyu.