Tsuntsaye na bata gonaki a Nijar

Tsuntsu jan baki
Image caption Tsuntsu jan baki

A jamhuriyar Nijar tsuntsaye jan baki sun fara lalata amfanin gona, a gundumar Malbaza da ke cikin jahar Tawa.

Rahotanni na nuna cewa kashi biyar cikin dari na amfanin gona sun salwanta a wasu sassan kasar, a sanadiyyar Barnar da tsuntsayen ke yi.

Ma'aikatar gidan gona ta yankin ta tabbatar da al'amarin, kuma ta ce tana iya kokarinta domin shawo kan matsalar.

Kusan a shekarun baya-bayan nan kasar ta Nijar, na fuskantar matsalolin tsuntsaye jan baki da farin dango da karancin ruwan sama, abin da kan jefa kasar cikin karancin abinci.