Kotu za ta fara shari'ar Pistorius a Maris

Oscar Pistorius a gaban kotu
Image caption Mai shigar da kara, Gerrie Nel na shirin maida shari'ar zuwa babbar kotu

Wata kotun majistire a Afrika ta Kudu, ta sanya watan Maris na badi, domin fara shari'ar zakaran motsa jiki Oscar Pistorius.

Ana zargin Oscar da kashe budurwarsa Reeva Steenkamp a watan Fabrairu, zargin da ya musanta, inda yace ya dauka wani ne ya yi masa kutse.

Har ila yau ana zargin dan wasan tseren da mallakar makami ba bisa ka'ida ba.

Pistorius ya bayyana a gaban kotun ranar Litinin fuskarsa a daure, yana kuka tare da rike hannun 'yan uwansa.