An kashe Abubakar Shekau- JTF

Image caption Abubakar Shekau

Rundunar hadin gwiwa ta JTF ta ce watakila shugaban kungiyar jama'atu ahlul sunna lil da'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram, watau Imam Abubakar Shekau ya mutu a sakamakon raunukan da ya samu.

A wata sanarwar da ta aika wa manema labarai da sa hannun laftanar kanal Sagir Musa tace, akwai yiwuwar raunin harbin bindiga ne ya yi ajalin Shekau.

JTF ta ce an raunata Shekau ne a wani artabun da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar ta Boko Haram a dajin Sambisa a ranar 30 ga watan Yuli.

Sanarwar ta kara da cewa an shigar da Shekau wani kauye, Amitchide a Kamaru domin a yi jinyarsa, amma ya mutu tsakanin ranar 25 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta.

'Bidiyo'

A ranar 13 ga watan Agusta ne Imam Abubakar Shekau ya fito a wani faifai bidiyo, inda ya ce kungiyar ce ke da alhakin kai wasu hare-hare da suka hada na Malam Fatori da Bama da Kuma Baga.

Haka kuma Shekau ya musanta batun kisan shi a wannan bidiyon.

Saidai sanarwar da JTF ta fitar ta yi ikirarin cewa ba Shekau ba ne a bidiyon, wani wanda ya ke kwaikwayonsa ne, domin karfafa wa 'ya 'yan kungiyar gwiwa.

Sanarwar ta JTF na zuwa ne a aranar da rundunar sojin Najeriya ta karbe ragamar tsaro a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa daga hannun rundunar hadaka ta JTF.

Karin bayani