An kashe 'yan sandan Masar 24 a Sinai

Garin Rafah na bakin iyakar Masar da Zirin Gaza
Image caption Garin Rafah na bakin iyakar Masar da Zirin Gaza

Jami'an tsaro a Masar sun ce an kashe akalla 'yan sanda 24 a wani kwanton-bauna a Sinai.

Ana dai zargin masu fafutukar Islama ne, suka afkawa motoco kirar bus-bus biyu, da 'yan sanda ke tafiya a ciki zuwa garin Rafah.

Hare-haren na karuwa a yankin Sinai, tun bayan tumbuke shugaban Masar Mohammed Morsi.

Fiye da jami'an tsaro 70 ne suka rasa rayukansu da wasu wadanda Masar ta kira 'yan ta'adda kimanin hakan ne suka mutu a makonni shida da suka wuce.