Amurka ta tattauna rage tallafi a Masar

Shugaba Obama da manyan jami'an fadar White House
Image caption Shugaba Obama da manyan jami'an fadar White House

Wasu manyan jami'an gwamnatin Amurka sun gana a Washington, domin tattauna batun rage tallafin da Amurkan ke baiwa kasar Masar, na dala biliyan daya da rabi.

Wakilin BBC ya ce gwamnatin Obama na fuskantar matsin lamba, domin rage kudaden tallafin da ta ke baiwa Masar.

Hakan ya biyo bayan kashe daruruwan magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi da gwamnatin Masar din dake samun goyon bayan sojin kasar ta yi.

Amurka ta kuma yi gargadin cewa, rashin sanya 'yan kungiyar a tattaunawar fayyace siyasar kasar, ka iya shafar tallafin wanda galibi ke zuwa hannun sojojin kasar.

Idan an jima a ranar Laraba ne Ministocin tarayyar Turai za su gana domin tattauna rikicin kasar, inda ake sa ran mai yiwuwa za su tattauna batun dakatar da baiwa kasar Masar din tallafi.

Majalisar Dinkin Duniya

Mai magana da yawun shirin lura da kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Elizabeth Throssel ta ce suna neman izinin aikewa da masu sa ido don duba halin da ake ciki a kasar ta Masar.

Ta ce daruruwan mambobin kungiyar Muslim Brotherhood ne aka bayyana cewa ana tsare da su, cikinsu kuwa har da wasu daga cikin shugabanninsu.

Fira Ministan kasar ta Masar dai ya kare matakin da jami'an tsaron kasar suka dauka, wajen kawo karshen zanga-zangar 'yan Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, na neman a dawo musu da hambararren shugaba Mohammed Morsi

A wata tatataunawa da kafar talabijin ta Amurka ABC, Hazem el-Beblawi ya ce kowa na bakin ciki da rasa rayukan da aka yi, amma kuma gwamnati ba ta da zabi a lokacin da aka kalubalance ta a tituna.

Ya kuma ce za a hukunta jagoran kungiyar ta 'yan uwa Musulmi Mohammed Badie kamar yadda dokar kasar ta tanada.

Sai dai a wani taron manema labarai, kakakin fadar White House Josh Earnest ya soki lamirin tsare Mr Badie.