'Akwai shakku game da kashe Shekau'

Image caption Abubakar Shekau

Masana sha'anin tsaro a Najeriya sun soma tsokaci kan sanarwar da Rundunar hadin gwiwa ta JTF ta fitar a kan cewar watakila an kashe Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

Sanarwar ta ce Shekau ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu yayin wata ba-ta-kashi da aka yi tsakanin watannin Yuli da farko watan Agusta.

Dr Bawa Wase, wani mai bincike kan tsaro ya ce " sai jami'an tsaron Najeriya sun nuna kabarin da aka binne Shekau, da kuma gwajin kwayoyin hallita na DNA kafin mutane su yarda da maganarsu".

Kawo yanzu gwamnatin Najeriya bata ce komai game da batun ba.

'Sharhin Andrew Walker'

Image caption Shekau da sauran 'yan Boko Haram

Idan har an tabbatar da labarin kashe Abubakar Shekau, lamarin zai zama wani abu sabo ga kungiyar Boko Haram.

Amma idan aka yi la'akari da abubuwan dake faruwa game da dakarun Najeriya, tabbas tsugune bata kare ba game da tashin hankali a arewa maso gabashin Najeriya koda an kashe Shekau.

Sojoji sun ce an kashe shi tsakanin 25 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta, amma kuma a cikin wannan lokacin da kuma makwannin da suka biyo baya, an kashe akalla mutane 70.

Mutane da dama a Najeriya basu yarda da abinda jami'an tsaro suke fadi ba game da rikicin, kuma galibin jama'a sun ce sai sun ga hujja kafin su yarda Abubakar Shekau ya mutu.

Karin bayani