Yoyon gurbataccen ruwa a Fukushima

Tashar nukiliya ta Fukushima
Image caption Ana fargabar kada gurbataccen ruwa ya malala zuwa teku da bai fi nisan mita 100 daga tashar ba

Gurbaccen ruwan da ke cikin wani tanki ya malala zuwa karkashin kasa, a tashar nukiliya ta Fukushima dake Japan.

Kamfanin wutar lantarki na Tokyo,Tepco ya ce an samu malalar tan 300 na gurbataccen ruwan dake dauke da tururin nukiliya mai yawan gaske a ranar Litinin.

Tun bayan lokacin da mahaukaciyar guguwa ta tsunami da kuma girgizar kasar da aka samu a shekarar 2011 da suka lalata tashar, ake samun yawan daukewar wutar lantarki da yoyon gurbataccen ruwa a tashar .

Mahaukaciyar guguwa

Tsunamin dai ta rushe abin dake sanyaya tukwanen nukiliyar, abin da ya sa uku daga ciki suka narke.

A wata sanarwa da Tepco ta fitar, kamfanin ya ce wani ma'aikaci ne ya gano yoyon a ranar Litinin.

Jami'ai dai sun bayyana malalar da cewa mataki na daya ne, wanda shi ne mafi kankanta a sikelin hukumar kasa da kasa dake sa ido a kan nukiliya da abubuwan da suka shafi tururinsa.

Wannan ne dai karon farko da Japan ta bayyana aukuwar lamarin, tun bayan bala'in na tsunami a shekarar 2011.