An soki Ghana kan kashe kudaden mai

Rijiyar hakar mai ta Ghana
Image caption Rijiyar hakar mai ta Ghana

An zargi gwamnatin Ghana da rashin kashe kudaden da take samu kamar yadda ya kamata, a kan samar da ababen more rayuwa da biyan basussuka da inganta harkar noma.

Wani sabon nazari da wata cibiyar sa ido a kan manufofin da suka shafi makamashi, ACEP dake Acca, babban birnin kasar ne ya bayyana hakan.

Nazarin ya nuna cewa cikin dala miliyan 287 na kudaden mai da kasar ta ware, domin kashewa a shekarar 2012, kashi 18 cikin dari na kudin an kashe su ne wajen gudanar da ofishin shugaban kasar.

Yayin da ba a kammala manyan ayyukan kasa kamar gina tituna da gadoji ba, saboda rashin sanya musu isassun kudade.