Ghana: An yankewa matashin jam'iyar NPP hukuncin kisa

Taswirar kasar Ghana
Image caption Taswirar kasar Ghana

Babbar Kotun Tamale a arewacin kasar Ghana, ta yankewa wani mai rajin kare hakkin matasa na jam'iyar adawa ta NPP hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.

An kuma yankewa wasu matasan na jam'iyar hudu hukuncin daurin shekaru 36 ko wannensu.

Hakan ya biyo bayan samun su da laifin hadin baki wajen aikata kisan kai a shekara ta 2009.

Tawagar masu taimakawa alkali mai mambobi bakwai, karkashin jagorancin Mai shari'a Lawrence Mensah ce ta tuhumi wadannan matasan biyar.

Matasan sun hada da Yahuza Yakubu, wanda shine aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar ratayewar, sai kuma Abibu Dgabana, Majeed Alhassan, Alhassan Sayibu da Imoro Gundaana.

Sai dai lauyan wadanda aka yankewa hukuncin Nana Obiri Boahene ya ce, hukuncin na da nasaba da siyasa, ya kuma ce za su daukaka kara.

An dai cafke wadannan mutanen ne a birnin Tamale, bayan wata arangamar siyasa da ta barke tsakanin matasan jam'iyar NDC da na NPP, a ranar 17 ga watan Fabrairun shekara ta 2009.

Hakan dai yayi sanadiyyar mutuwar matashin jam'iyar NDC mai mulkin kasar.

An kuma kone gidaje 27, motoci, babura da sauran dukiyoyin jama'a a yankunan Gumbihini, Choggu da sauran kauyukan dake kewaye da birnin na Tamale.