An kashe mai yaki da 'yan camfi

Image caption Dabholkar ya sha kalubalanatar malaman duba a India

'Yan sanda a yammacin kasar India sun ce an kashe wani mai fafutukar ganin an kafa dokokin yaki da camfi da tsafi.

'Yan sandan sun ce wadansu 'yan bidiga da ba a san ko su wanene ba ne suka harbe dan fafutukar mai suna, Narendra Dabholkar, lokacin da yake tafiya a kan titin birnin Pune.

Mista Dabholkar, wanda ke da shekaru 71 a duniya, ya kwashe shekaru da dama yana fafutukar ganin al'umar kasar sun sauya tunaninsu game da camfi.

Ya sha kalubalantar manyan 'yan tsubbu da malaman-duba na kasar ta India game da ikirarin da suke yi cewa suna yin abin da ba ya yiwuwa, da kuma shelar ganin an daina amfani da dabbobi wajen tsafi.