Ruto zai dinga halartar zaman kotu- ICC

Image caption Mataimakin Shugaban Kenya, William Ruto

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa- ICC ta yanke hukuncin cewa, daga yanzu mataimakin shugaban kasar Kenya zai rinka halartar duk zaman da za ayi a kan tuhumar da ake masa ta laifin cin zarafin bil-adama.

Wannan mataki dai ya biyo bayan bukatar hakan da mai shigar da karar ta yi kan cewa, Mista William Ruto ya rinka halartar zaman kotun da ake a Hague har sai an yanke hukunci a kan daukaka karar.

Za a fara sauraron karar daga ranar goma ga watan Satumba, kuma ba a bayyana ranar da za a yanke hukunci ba.

Ana tuhumar MistaRuto da hannu a cikin barkewar babban rikicin kasar da ya biyo bayan zaben da aka yi a shekara ta 2007.

Akwai kuma sauran mutane hudu da ake tuhumar su tare da aikata irin wannan laifi, cikin har da Shugaba Uhuru Kenyatta.

Karin bayani