'Yan Uwa Musulmi sun yi tur da tsare Badie

Image caption Muhammed Badie

Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta yi Allawadai game da tsare shugabanta, Muhammed Badie.

Kakakin kungiyar ya ce tsare shugaban wani yinkuri ne da ya saba da tsarin juyin juya halin da aka yi a shekara ta 2011, lamarin da ya kifar da gwamnatin Hosni Mubarak.

An kama Mista Badie ne a cikin dare a kusa da wuraren da aka kafa sansanonin da jami'an tsaro suka tawarwatsa, abinda ya janyo hasarar rayuka da dama.

A taron manema labarai, kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta bukaci magoya bayanta su ci gaba da zanga-zanga kan bukatar a maidoda hambararren shugaban kasar Muhammed Morsi kan mulki.

Kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi ta nada Mahmoud Ezzat a matsayin shugaba na riko.

'Zargi a kan Morsi'

Masu shigar da ƙara a Masar sun gabatar da sabbin tuhume-tuhume a kan hamɓararren shugaban ƙasar mai ra'ayin addinin musulunci Muhammad Morsi.

Masu gabatar da kara sun ce, za'a tuhumi Morsi ne da laifin rura wutar rikici.

Tuhume-tuhumen na da alaka da rasuwar mutane da dama yayin zanga-zangar kin jinin gwamnatin Morsi da aka gudanar a kofar fadar shugaban kasa a watan Disamban shekarar da ta gabata.

Karin bayani