An kashe mutane hudu a Gamboru Ngala

Image caption Mayakan Boko Haram

Rahotanni daga garin Gamboru Ngala a jihar Borno na cewar wadansu matasa da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane hudu tare da raunata wasu takwas a wani hari da suka kaddamar a daren ranar Talata.

Wani mazaunin garin, ya tabbatarwa BBC cewar an yi jana'izar mutane hudun sannan wadanda suka samu raunuka suna jinya asibiti.

Mutumin wanda bai son a bayyana sunansa ya ce, 'yan Boko Haram din sun yi amfani da wata dabarar janyo hankalin 'yan garin ta hanyar busa asur kafin su bude musu wuta.

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labarin saboda rashin wayar sadawar a jihar ta Borno.

Wannan lamarin ya faru ne kwanaki biyu ba yanda jami'an tsaro suka sanarda cewa watakila Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya mutu sakamakon raunukan da ya samu na harbin bindiga.

Karin bayani