Daukaka kara game hukuncin kisa a Ghana

Image caption Shugaban Ghana, John Dramani

Lauyan matashi dan jam'iyyar adawa ta NPP a Ghana, ya ce za su daukaka karar hukuncin kisan da aka yanke wa Yakubu Yahuza.

A cewar Lauyan, babu adalci a shari'ar.

A ranar Talata ne aka yanke wa Yahuza hukuncin kisa ta hanyar ratayewa, bisa hannu a kashe Rashid Alhassan na jam'iyyar NDC mai mulkin kasar a shekara ta 2009 lokacin da masu hamayya da juna suka fafata a arewacin Ghana.

Tun shekarar 1993 ba a yi amfani da hukuncin kisa ba a Ghana, abinda ya janyo aka samu daidaito a tsarin demokradiyar kasar.

An kuma yankewa wasu matasan na jam'iyyar hudu hukuncin daurin shekaru 36 a gida kaso ko wannensu.

Matasan da aka yankewa hukuncin su ne Abibu Dgabana, Majeed Alhassan, Alhassan Sayibu da kuma Imoro Gundaana.

Karin bayani