Kotu na shirin bada belin Mubarak

Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak
Image caption Ana sa ran mai gabatar da karar zai kalubalanci bada bailin Mubarak abin da zai kawo jinkirin sakin shi

Wata kotu a Masar za ta yanke hukunci a kan ko za ta bada belin tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak.

Mr. Mubarak dai ya daukaka kara ne a kan tsare shi da ake yi, bisa tuhumarsa da aikata cin hanci da rashawa.

Haka kuma ana tuhumar tsohon shugaban, da hada baki wajen kashe masu zanga-zanga, a lokacin da aka yi juyin-juya-halin da ya kawo karshen mulkinsa.

A watan Yunin shekarar 2012 ne aka samu Mr. Mubarak mai shekaru 85 a duniya da hannu a kashe masu boren, inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Karin bayani