Takun saka a gwamnatin hadakan Nijar

Shugaban kasar Nijar, Muhamadou Issoufou
Image caption Shugaban kasar Nijar, Muhamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar bangaren shugaban kasar, da na shugaban majalisar dokoki, malam Hama Amadu na tattaunawa domin warware takun sakar dake tsakaninsu.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban jam'iyyar Moden Lumana ta dauki matakin kaurace wa ayyukan gwamnati a karshen makon jiya.

Hakan ya biyo bayan rashin gamsuwar da Jam'iyar ta Lumana ta yi, da mukaman da aka bata a sabuwar gwamnatin hadakar.

Sai dai wasu jam'iyyu biyu da ke cikin kawancen MRN mai mulki, sun jaddada goyon bayansu ga shugaban kasar Mohamadou Issoufou.