Jam'iyyar APC ta fitar da manufofinta

Image caption Tambarin jam'iyyar APC

Sabuwar jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta fitar da manufofinta a Abuja babban birnin tarayyar kasar.

Manufofin dai sun hada da samar da aikin yi ga matasa, da kawar da cin hanci da rashawa, da gyara makarantu a fadin kasar.

Mataimakin Sakataren riko na APC, Malam Nasir El-Rufai ya ce jam'iyyarsu za ta fidda kasar daga matsaloli da take fuskanta idan har talakawan Najeriya suka zabesu a shekara ta 2015.

A cewar El-Rufai, wannan ne karon farko a tarihi siyasar Afrika da jam'iyyun adawa uku suka dunkule waje guda.

Tun daga shekarar 1999 da aka koma mulkin demokradiyya a Najeriya, jam'iyyar PDP ce jan ragamar kasar.

Masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin cewar zaben shekara ta 2015, zai kasance cike da sarkakiya gannin yadda aka ja zare tsakanin 'yan adawa na APC da kuma 'yan PDP masu mulkin kasar.

Karin bayani