An fara shari'ar Bo Xilai a China

Image caption Bo Xilai ya bayyana gaban kuliya

An fara shari'ar tsohon jigo na jam'iyyar kwaminisanci ta China, Bo Xilai, wanda ake zarginsa da karbar cin hanci na miliyoyin dala.

Ya musanta zargin karbar toshiyar baki.

Mista Bo kuma na fuskantar tuhuma a kan yin rufa-rufa game da kashe wani dan kasuwa na Birtaniya, Neil Heywood, da matarsa ta yi.

Hukumomi sun nuna hoton Mista Bo wanda ya shafe watanni 17 ba a ganshi a bainar jama'a ba, a cikin wata kotu a birnin Jinan da ke gabashin kasar.

Tuni dai aka kunyata dan siyasar sannan aka cire shi daga mukaminsa.

Karin bayani