Za a gudanar da zanga-zanga a Masar

Wata mai goyon bayan kungiyar 'yan uwa musulmi cikin jini
Image caption kungiyar 'yan uwa musulmi sun bukaci magoya bayansu su fito a yau ranar shada

Kungiyar 'yan uwa musulmai a kasar Masar ta yi kira ga magoya bayanta da su gudanar da zanga-zangar da suka kira ta ranar yin shahada a ranar bayan sallar juma'a.

Wakilin BBC a yankin gabas ta tsakiya, ya ce magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmin sun girgiza da irin matakan amfani da karfi da jami'an tsaron kasar suka yi.

Wajen tarwatsa su daga sansanonisu da suka kafa na zaman dirshan a makon da ya gabata.

Kuma dokar hana yawon dare da gwamnatin rikon kasar ta kafa na yin tasiri.

Karin bayani