Kamaru ta rufe iyakarta da CAR

Image caption Rashin jituwa ya sa Kamaru ta rufe iyakarta da Afrika ta tsakiya

Hukumomi a gabacin Kamaru sun rufe iyakarsu da Jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Gwamnatin dai ta dau wannan matakin ne bisa dalilin kisan wani dan sanda da aka tuhumi wasu sojojin kungiyoyin SELEKA da aikatawa.

Hakan ya biyo bayan cacar bakin da jami'an kasashen biyu suka yi ne sakamakon abinda sojojin SELEKA suka kira wasa da hankalin da jami'an tsaron Kamaru suka yi musu.

Lamarin ya faru lokacin da sojojin Seleka suke komawa kasarsu bayan sun shiga kasar ta Kamaru domin biyan wasu bukatu.

A baya can dai an yi ta samun takaddama tsakanin jami'an tsaron kasashen biyun bisa ga dalilai daban-daban.

Karin bayani