An sallami Mubarak daga gidan kaso

Hosni Mubarak
Image caption Hosni Mubarak

An sallami tsohon Shugaban kasar Masar Hosni Mubarak daga gidan kurkuku, bayan ya shafe sama da shekaru biyu ana tsare da shi.

Wani jirgi mai saukar ungulu ne ya dauki Mista Mubarak daga gidan kason Tora da ke birnin Alkhahira inda ake tsare da shi.

Duk da wannan saki, Mista Mubarak yana fuskantar wata tuhumar a kan samun hannu wajen kisan masu zanga zanga a lokacin boren da ya yi sanadiyar saukarsa daga kan karagar mulki kusan shekaru biyu da suka wuce.

'Daurin talala'

Mahukuntan sojin kasar Masar sun bada umarnin a ci gaba da yiwa Hosni Mubarak daurin talala, bayan da wata kotu ta bada izinin sakinsa bisa wani sharadi, tun da ya yi zama na tsawon lokacin da ya kamata yayi a gidan kaso gabanin a yi masa shari'a.

Ana ganin sakin Mubarak a matsayin wata alama dake nuna cewar sojoji na koma wa tsohon tsari kafin juyin-juya halin kasar.

A halin yanzu kasar Masar na karkashin dokar ta baci ne sakamakon zubar da jinin da ya biyu bayan kawar da magoya bayan hambararren Shugaban kasar Muhammed Morsi.

Tuni aka tsare daruruwan magoya bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ciki hadda shugabanta, Mohammed Badi bisa zargin tunzura tashin hankali.