'Gwamnatin Nijar ta ki cika alkawari'

Image caption Mutanen sun ce gwamnati ba ta cika mu su alkawari ba

A jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar, mutanen da ambaliyar ruwan Komadugu ta shafa sun ce gwamnatin jihar ba ta cika musu alkawarin da ta yi ba na gina musu gidaje.

Wadansu daga cikinsu da ke zaune a unguwar Bagara sun ce gwamnati ta ba su kudaden gini CFA 55.00 sai dai ba ta samar mu su da filaye ba kamar yadda ta yi alkawari.

Hukumomin Birnin na Diffa dai sun ce akwai wuraren da za a ba mutanen sai dai ana so a kammala wasu ayyuka ne a wuraren.

Mazauna birnin dai sun yi fama da ambaliyar ruwan ne a bara, lamarin da ya kai ga gwamnati yin alkawarin ba su filayen da za su gina gidaje.

Karin bayani