PDP za ta yi taron gaggawa

Image caption PDP na kokarin warware matsalolinta

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta kira wani taron gaggawa wanda za a yi a yau Alhamis a babban birnin Tarayya Abuja.

Kodayake dai jam'iyyar ba ta bayyana abubuwan da taron zai tattauna ba, wasu majiyoyi sun tabbatar da cewar rikicin da ya kunno kai kan babban taron da jam'iyyar ta shirya yi domin zaben shugabannin tsakanin ta ake son warware shi.

Jamiyyar dai ta saka ranakun 24 da 31 na wannan watan don yin babban taron ta.

Akwai dai rashin jituwa tsakanin wasu gwamnonin da suke marawa Shugabancin Amaechi a matsayin shugaban Kungiyar gwamnonin Kasar da kuma Shugaban Jamiyyar PDP Bamanga Tukur.

Karin bayani