Gina layin dogo daga Kamaru zuwa Chadi

Image caption Layin Dogo

A wani mataki na karfafa hulda a tsakaninsu, kasashen Kamaru da Chadi sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya, ta shumfuda layin dogo daga birnin Ngaoundere a Kamaru zuwa N'Djamena, babban birnin Chadi.

Wannan yunkuri don habaka kasuwanci a tsakaninsu ne, da kuma sawwaka jigilar kaya daga tashar jirgin ruwan birnin Douala zuwa kasar Chadi.

Da yake Chadi ba ta yi iyaka da teku ba, kashi tisi'in cikin dari na kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen duniya, ta tashar jiragen ruwan Kamaru suke biyowa.

'Yan kasuwa musamman na Chadi za su yi murnar wannan matakin ganin cewar zai saukaka musu harkokinsu na jigilar kayayyaki zuwa cikin kasarsu.