Congo: Ana luguden wuta a birnin Goma

Image caption Dakarun Majalisar Dinkin Duniya

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun kaddamar da luguden wuta a yankunan da 'yan tawaye keda karfi a kusa da birnin Goma.

Dakarun na maida martani ne sakamakon hare-haren da 'yan tawayen M23 suka kai a Goma a ranar Alhamis lamarin daya hallaka fararen hula biyar.

Kakakin 'yan tawayen M23 ya shaidawa BBC cewar basu kai hari a birnin ba, inda ya zargin sojojin da takalar fada.

Ana shirin tura dakaru na musamman zuwa yankin don murkushe 'yan tawaye.

An baiwa dakarun alhakin tabbatar da 'yan tawaye sun anjiye makamansu.

Karin dakaru 3,000 ne za su hade da tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta wanzar da lafiya mai suna MONUSCO inda a jumlace za a samu dakaru kusan 18,000.

Karin bayani