'Yan Boko Haram sun kashe mutane 44'

Image caption 'Yan Boko Haram

'Yan bindiga sanye da kayan soji sun kashe mutane akalla 44 ta hanyar bude musu wuta a daidai lokacin da suke fitowa daga Masallaci a kauyen Dumba dake kusa da Baga a jihar Borno.

Kakakin rundunar tsaron Najeriya, Birgadiya Janar Chris Olukolade ya shaidawa BBC cewar 'yan Boko Haram ne suka kaddamar da harin bisa zargin jama'ar da kin basu hadin kai.

Lamarin ya auku ne a ranar Litinin amma ba a samu labarin ba sai ranar Juma'a saboda an katse layukan salula a ɗaukacin jihar ta Borno.

Wata majiya ta bayyana cewar 'yan Boko Haram din sun yin kwantan ɓaune ne suka jira mutanen suka fito daga Masallaci bayan sallar asuba sannan suka buɗe musu wuta.

A farkon wannan watan, 'yan Boko Haram din sun kai hari a wani Masallaci a Konduga inda suka hallaka musulmi 44 tare da raunata wasu 12.

Karin bayani