Ambaliyar ruwa ta shafe kauyuka 18 a Bauchi

Image caption Mutum daya ya mutu sakamakon ambaliyar ruwan

Kauyuka 18 ne suka shafe sanadiyar ambaliyar ruwan da aka yi ranar Alhamis a karamar hukumar zaki ta jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya.

Hukumomi a karamar hukumar sun tabbatarwa BBC cewa wani mutum ya mutu, sannan mutane biyu suka samu raunuka sakamakon ambaliyar ruwan.

Mazauna kauyukan dai sun ce ba su san inda za su sanya kawunansu ba bayan aukuwar ambaliyar ruwan, suna masu yin kira ga hukumomi da su tallafa musu.

Hukumomin sun yi alkawarin tsugunar da mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a wadansu wuraren.

An kwashe kwanaki da dama ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin, amma lamarin ya ta'azzara ne ranar Alhamis inda gidaje suka yi ta rushewa.

Karin bayani