An yi wa wata 'yar jarida fyade a Indiya

Masu zanga-zanga a kan yi wa mata fyade a Indiya
Image caption A watan Disambar 2012, wasu maza sun yi wata daliba fyade a Delhi, abin da ya yi ajalinta, lamarin kuma ya janyo bore

Wasu maza biyar sun yi wa wata 'yar jarida dake daukar hotuna, mai shekaru 23 fyade a birnin Mumbai na Indiya.

Matar ta je aiki ne da maraicen ranar Alhamis, a lokacin da gungun suka yi mata fyade, kuma a halin yanzu tana asibiti tana jinyar raunukan da ta samu.

Lokacin da lamarin ya faru dai tana tare ne da wani abokin aikinta, amma gungun suka lakada masa duka.

Kawo yanzu 'yan sanda sun kama daya daga cikin wadanda ake zargi.

Matsalar yi wa mata fyade a Indiya na karuwa, musamman ma a baya-bayan nan.