Rasha na zargin 'yan adawa a Syria

Image caption Amfani da makamai masu guba laifi ne gagarumi

Kasar Rasha ta ce akwai shaida mai karfi da ke nuna cewa 'yan tawayen Syria ne ke da alhakin kai harin amfani da makamai masu guba a Ghouta kusa da babban birnin kasar Damascus.

A lokaci guda kuma Moscow ta yi kira ga Shugaba Assad ya bada hadin kai ga binciken Majalisar Dinkin Duniya kan lamarin.

Masu adawa da Gwamnatin shugaba Assad na cewa za su taimakawa jami'an binciken makamai masu guba na Majalisar Dinkin Duniya don gudanar da binciken.

Shugaba Obama a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na CNN ya ce zargin amfani da makamai masu guba laifi ne mai girman gaske.

Karin bayani