Sojan Amurka na fuskantar hukuncin kisa

Image caption Sojan Amurka Nidal na jiran hukunci

Sojan Amurka mai kula da masu tabin hankali, Major Nidal Hasan an same shi da laifin kisan mutane 13 da kuma raunata mutane fiye da 30 bayan da ya bude wuta a sansanin sojin Ford Hood dake Texas a shekara ta 2009.

Amsa laifinsa da ya yi zai iya fuskantar hukuncin kisa.

Manjo Nidal Hasan ba a bashi lauyoyin sojoji ba da za su kare shi ba; ya kare kansa da kansa a shariar.

Haka kuma bai kirawo wasu shaidu ba kuma bai yi jawabi a kotun ba; ko kuma kammala jawabai gaban mai sharia.

Ya dai amsa laifinsa.

A yanzu dai za a fara matakin yanke hukunci ne a shariar.

Karin bayani