'Yan tawayen Syria ne suka kai hari'

Wani majinyaci a Syria
Image caption Daruruwan mutane ne suka mutu a sanadiyyar hari da makamai masu guba, ranar Laraba

Rasha ta ce shaidar da ke kara fitowa fili tana nuna cewa 'yan tawayen Syria ne ke da alhakin hari da makami mai guba da aka kai garin Ghouta, kusa da Damascus, babban birnin kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen Rashar ta ce tana ganin an harba rokan da ke dauke da sinadarin mai guba ne daga yankin da 'yan tawayen suke.

Sannan zargin gwamnati a kan harin, 'yan tawayen ne suka soma yin sa a shafukan intanet tun ma kafin shi harin ya auku.

'Hadin Kai'

Gwamnatin Rasha ta yi kira ga Shugaba Assad na Syriar da ba da hadin kai masu binciken makamai masu guba.

Shugaban Amurka Barack Obama shima ya ce kasarsa na kokarin tabbatar da ko an yi amfani da makamai masu guba a Syria, kuma idan da gaske ne to hakan zai ja hankalin Amurkar.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya ce kin barin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya su ziyarci kusa da wuraren da aka kai harin, na nuna cewar gwamnatin Syria na kokarin boye wani abu.

Karin bayani