Mutane 27 sun hallaka a Tripoli na Lebanon

Image caption Bakin hayaki ya turnuke sama

Mutane akalla ashirin sun mutu sakamakon fashewar wasu abubuwa masu karfi guda biyu a kusa da Masallaci a birnin Tripoli na kasar Lebanon.

Lamarin kuma ya janyo mutane fiye da 350 sun samu raunuka.

Hotunan talabijin sun nuna yadda bakin hayaki ya turkune sararin samaniya a birnin.

Wakilin BBC a Lebanon ya ce bisa dukkan alamu wani babban malamin sunna aka kitsa kaiwa hari jim kadan bayan sallar Juma'a.

Malamin, Salem Raf'ee yana baiwa maza kwarin gwiwa su shiga a yi yaki da gwamnatin Syria tare dasu.

A makon daya gabata ne, wata mota makare da bam ta hallaka mutane 27 a lardin 'yan Shi'a dake Beirut babban birnin kasar ta Lebanon.

Karin bayani