Kano: An yi taron nuna goyon baya ga Morsi

A Najeriya dubban musulmai sun taru a Kano da domin nuna goyon bayan su ga hamɓarerren shugaban Masar Muhammad Morsi.

Wadanda suka taru sun kuma yi Allah wadai da kisan daruruwan masu zanag zanga a Masar.

Kungiyoyin musulunci karkashin kungiyar jaddada musulunci wato Jama'atu Tajdidil Islam ne suka shirya taron wanda malamai daga bangarori daban daban suka halarta.

Masar dai tana fama da rikici tun bayan tumɓuke gwamnatin Morsi.