Kungiyar Likitoci ta MSF ta yi tsokaci kan harin guba a Syria

Asibitin MSF
Image caption Asibitin MSF

Kungiyar agaji ta likitoci, Medicins San Frontieres ta ce, wasu asibitoci uku da suke taimakawa a Damascus babban birnin Syria sun duba mutane dubu uku da dari shidda dake fama da alamun harbuwa da guba, kuma fiye da dari uku da hamsin daga cikin mutanen sun mutu.

Kungiyar agajin ta ce, mutanen da aka duba din sun je asibitin ne ranar 21 ga watan Agusta, wacce ita ce ranar da 'yan adawar Syria suka sanar da cewa, anyi amfani da makamai masu guba wajen kai hari akan 'yan tawaye.

Wakiliyar BBC ta ce, kafofin yada labaran gwamnatin Syria sun ce, akwai sabbin shaidu dake nuna cewa, 'yan tawaye ne suka yi amfani da makamai masu guba wajen kai harin.

Karin bayani