Shari'ar Bo Xilai ta shiga rana ta biyar

Bo Xilai a kotu
Image caption An dai taba ba da suna Bo Xilai a ciki wadanda za a zaba 'yan kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis watau Politburo.

Ana saran tsohon jigon siyasar kasar Sin din nan wanda ake yiwa shara'a kan zargin cin hanci da rashawa ya bayar da bahasinsa na karshe a yau.

Masu aiko da rahotanni sun ce jama'a kasar zasu sa ido sosai kan wannan muhawarar karshe a sharia'r da tafi kowace zafafa fagen siyasar kasar a cikin shekaru gommai.

Mr. Bo, tsohon jami'in babban kwamitin Jam'iyyar Kwaminis mai mulki a yankin Chongqin, ya musanta zarge-zarge karbar cin-hanci da anfani da mukaminsa ta hanyar da bata dace ba da ake masa, tare da yin kakkausar suka ga tsohon abokin huldarsa wanda ya bayar da shaida a kansa.

An dai hana kafafen watsa labarai na kasashen wajen isa inda ake sharia'ar, amma kotun wadda ke birnin Jinan ta kan sa bayanan shara'ar a shafin intanit na Weibo akai-akai.

Karin bayani