Ana bore a Congo kan rikici a Kasar

Image caption Ana zanga-zangar kyamar rikici a Congo

Daruruwan mutane sun bazama a kan titunan garin Goma na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo suna boren nuna rashin amincewa da fadan da ake gwabzawa a kasar.

Mutane akalla uku aka ba da rahoton an kashe lokacin da wasu manyan harsasai suka fada wani gida dake birnin a safiyar Asabar.

Sai dai kawo yanzu ba a tantance wanda ke da alhakkin harba manyan harsasan na baya bayan nan ba; amma masu zanga zangar sun nuna fushin su ga yakin; da yawansu kuma sun dora laifin ne kan rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Fadan dai ya barke ne a gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo saboda wata sabuwar rudunar tsoma baki ta Majalisar Dinkin Duniya da aka tura don kakkabe 'yan tawayen.

Karin bayani