Hukumar Alhazai ta yi gargadi kan cutar mura

Image caption An yi gargadin yiwauwar kamuwa da cuta a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Nigeria ta yi gargadi game da hadarin cutar murar Coronavirus ga maniyyata aikin Hajjin bana.

Wannan cuta a cewar hukumomin Alhazan ta bulla ne a yankin Gabas ta tsakiya kuma ta na cigaba da yaduwa a kasashen Larabawa da suka hada da Saudi Arabia.

A wani taron manema labarai da ta gudanar a Abuja, hukumar ta shawarci maniyyata aikin hajjin bana masu fama da ciwon suga da cutar HIV da masu dauke da duk wani nau'in cuta wanda ke rage karfin garkuwar jiki da su hakura da aikin Hajjin bana.

Ita dai wannan cuta ta Coronavirus kawo yanzu ba ta da magani, sai dai hanyoyin kiyaye kamuwa da ita.

Karin bayani