Jirgin kasa da kasa ya fara tashi a Enugu

Image caption Najeriya ta fara tashin jiragen kasa da kasa a Enugu

A Najeriya, a yammacin jiya Asabar ne; aka fara gudanar da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa a babban filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke birnin Enugu.

A 'yan watannin baya ne dai aka kara inganta filin jirgin saman don ya dace da irin wannan harkar sufurin, bayan da aka daukaka matsayinsa zuwa babban filin jirgin sama na kasa da kasa a shekaru uku da suka gabata.

Jama'ar yankin kudu maso gabashin Najeriya dai na ganin hakan wani kyakkyawan ci gaba ne, wanda zai rage wahalhalun tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da komowa gida Najeriya daga waje.

Enugu dai gari ne da ya tumbatsa wajan gudanar da harkokin kasuwanci a yankin kudancin kasar.

Karin bayani