Sabuwar takaddama kan kidaya a Najeriya

Image caption Alkaluman kidayar na 2006 dai sun nuna jihar ta Kano na da mutane miliyan 9.4.

Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta ce ba za ta shiga kidayar jama'a da za'a yi a kasar ba a shekara ta 2016.

''Mu ba zamu taba yarda wani Festus Odumegwu ko wakilansa su zo su kirga mu ba.'' Inji Gwamnan Jahar Rabiu Musa Kwankwaso a wata hira da BBC.

Kwankwaso na mayar da martani ne ga kalaman da aka danganta da shugaban Hukumar, Mr. Odumegwu na cewa kidayar jama'ar ta 2006, wacce ta nuna Kano ta fi kowace jiha yawan al'umma, ba sahihiya ba ce.

Tun a shekarar ta 2006 dai jahar Legas ta yi watsi da sakamakon kidayar da ya nuna ita ce ta biyu a yawan jama'a.

Yawan al'umma na daga cikin manyan abubuwan da ake la'akari da su a Najeriya, wajen rabon arzikin kasa tsakanin jahohin kasar 36.

Karin bayani