Syria ce ta kai harin makamai masu guba —Amurka

Image caption Amurka da Birtaniya na shirn daukar mataki kan Syria

Manyan masu ba wa shugaba Obama shawara kan harkokin tsaro sun bashi cikakken bayanai kan matakan da za a iya dauka a matsayin martani kan harin makamai masu guba da aka kai a Syria.

Mr Obama ya kuma tuntubi Firai Ministan Birtaniya David Cameron, wanda ofishinsa ya nuna matukar damuwa da harin gubar da aka kai.

Ya ce alamun da ake dada gani na nuna cewa gwamnatin Syria ta kai harin makamai masu guba akan 'yan kasarta.

Gwamnatin Amurka ta ce sakataren harkokin wajenta John Kerry, ya shaidawa takwaransa na Syria cewa ya kamata a ce an ba wa masu binciken makamai masu guba na Majalisar Dinkin Duniya damar shiga yankin da aka kai harin a birnin Damascus.

Taron da Obama ya yi da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro a Amurka ya zo ne a lokacin da Barack Obaman ya tattauna da Firai Ministan Birtaniya David Cameron kan kalubalen tsaro da ke fuskantar Amurka da Burtaniya, har da batun ci gaba da rikici a Syria.

Sai dai duk da wadannan kalaman da Amurkar ke yi cewa gwamnatin Syria na da alhakkin harin amfani da makamai masu guba, Gwamnatin Shugaba Assad na cewa bata da hannu kuma ta dage cewa 'yan tawayen ne suka kai harin.

Karin bayani