An zargi Assad game da makamai masu guba

Image caption Wakilin BBC a Washington ya ce mai yiwuwa Amurka na share fage kai wa Syria harin soji ne.

Sakatare harkokin wajen Amurka, John Kerry ya yi tur da abin da ya kira amfani da makamai masu guba da gwamnatin Syria ta yi, ta yadda ba za a iya musantawa ba.

Mr. Kerry ya ce Shugaba Obama ya yi amanna cewa gwamnatin Syria za a kama da alhakin amfani da makamai mafiya hadari a kan mutanen da suka fi kowa rashin kariya.

Ya kara da cewa nan da kwanaki masu zuwa shugaban zai yanke shawarar matakai na gaba da zai dauka.

Amma Shugaba Putin na Rasha ya shaida wa Farai Minista, David Cameron na Birtaniya cewa babu shaidar da ke nuna cewa, an kai hari da makamai masu guba a Syria.

Karin bayani