Boko Haram: Iyalai na Kaura zuwa Chadi

Farmakin sojin ya soma ne tun a watan Mayu sa'adda shugaban kasar ya ayyana dokar-ta-baci a jahohin uku inda kungiyar ke da sansanoninta.
Bayanan hoto,

Farmakin sojin ya soma ne tun a watan Mayu sa'adda shugaban kasar ya ayyana dokar-ta-baci a jahohin uku inda kungiyar ke da sansanoninta.

Daruruwan iyalai a arewa-maso gabascin Najeriya na kwarara zuwa cikin makwabciyar kasar Chadi domin guje wa farmakin sojojin kasar ke kai wa mayakan kungiyar Boko Haram.

Rahotanni sun ce yanzu haka daruruwan iyalan 'yan gudun hijirar sun isa a garin N'Gbouboua dake kudu masu gabashin kasar daura da tafkin Chadi.

'yan gudun hijirar sun hada da 'yan kasashen Nijar da Kamaru da kuma kasar ta Chadi da ke zaune a can; sai dai galibinsu 'yan Najeriya ne.

Wani mazaunin babban birinin kasar ya shaidawa BBC cewar wasu 'yan gudun hijirar sun isa har can N'jamena.

''Akwai 'yan gudun hijira masu dimbin yawa da suka fito daga Maiduguri da Yobe da sauran jahohin da abin ya shafa. Tun lokacin da aka soma shiga gida-gida tare da samari suna neman duk mutumin da suka ga alamun cewa dan Boko Haram ne, to lokacin ne suka kwararo suka shigo har nan birnin N'jamena.'' In ji shi.