Hodar ibilis na gaggawar sauya tunani

Image caption Masana sun ce amfani da hodar ibilis na sauya tsarin kwakwalwa

Masana a Amurka sun ce shan hodar ibilis ka iya sauya tsarin kwakwalwar bil adama cikin sao'i kadan a wani matakin farko na kamuwa da masifar shan miyagun kwayoyi.

Wani rahoto da aka wallafa a mujallar kimiyya mai suna Nature Neuroscience, ya ce gwajin da aka yi a kan dabbobi ya nuna sababbin tsare-tsare masu alaka da yadda ake iya koyar wani abu da kuma yadda tunani ke sauyawa bayan an sha miyagun kwayoyi.

Bera wanda ke da akasarin sauye-sauye a kwakwalwarsa ya nuna sha'awa sosai ga hodar ibilis.

Masana sun bayyana hakan da cewa kwakwalwarsa tana da matukar shaukin koyon wani abu.

Wata tawagar masana daga jami'oin California da ke Berkeley da ta San Francisco sun yi nazari kan wasu kasusuwa da ke kumbura a kusa da kwakwalwa masu suna dendritic spines.

Kasusuwan suna yin tasiri sosai a kan yadda ake yin tunani.

Neman hodar ibilis

Wuraren da ake yin tu'ammali da miyagun kwayoyi suna taka muhimmiyar rawa a kan yadda ake kamuwa da masifar shan miyagun kwayoyi.

A gwajin da masanan suka yi, sun kyale berayen su yi amfani da wasu kwanuka guda biyu, kowanne dauke da abubuwa masu kanshi daban.

Da zarar sun dauki abin da suke so sai a yi musu allura mai dauke da hodar ibilis.

Masanan sun yi amfani da na'ura domin ganin yadda kwakwalwar berayen ke yin aiki, inda suka gano irin tasirin da hodar ibilis ke aiki a kwakwalwar tasu.

Karin bayani