'Fargabar yaduwar cututtuka a Najeriya'

Image caption An baiwa cutar shan inna fifiko

Hukumar kula da lafiya a matakin farko a Najeriya ta nuna damuwa game da yiwuwar yaduwar wasu cututtuka masu hallaka kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar.

Cututtukan sun hada da Bakon Dauro da shawara da kuma Sankarau.

Hukumar a wani taron manyan ma'aikatan gwamnatin arewacin Najeriya a Kaduna, ta ce dole ne a dauki matakan gaggawa.

Hukumar ta ce hakan ya biyo bayan mayar da hankalin da hukumomin lafiya ke yi ne wajen kokarin kawar da cutar Shan-Inna ko kuma Polio a kasar.

A cewarta akwai bukatar jihohin kasar su maida hankali wajen bada alluran rigakafin sauran cututtukan da ke hallaka kananan yara baya ga cutar shan-innan.

Karin bayani